in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Najeriya: Harin Bam ya hallaka mutane 11 a wani masallaci
2018-07-23 19:50:50 cri
A kalla mutane 11 ne suka rasu kana wasu 8 suka jikkata, sakamakon harin kunar bakin wake da wani mahari ya kaddamar, a wani masallaci dake Konduga dake jihar Borno a arewa maso gabashin Najeriya.

Wani ganau ya shaidawa majiyar mu cewa, maharin ya shiga masallacin ne da Asubahin Litinin din nan, inda ya saje da masallata, kafin ya tarwatsa abun fashewar dake jikin sa.

Yunusa Bala, wanda ya tsallake rijiya da baya a harin, ya ce dukkanin wadanda suka rasu masallata ne da suke shirin yin sallar Asuba, a lokacin da wannan lamari ya auku.

Bala ya ce mutane 7 sun rasu ne nan take cikin masallacin, yayin da wasu mutanen 2 suka rasu a harabar masallacin. Kaza lika wani mutum guda ya rasu yayin da aka garzaya da shi asibiti. An dai kai da yawa daga wadanda suka jikkaya asibitin koyarwa na jami'ar Maiduguri fadar mulkin jihar ta Borno, wanda ke da nisan kilomita 43 daga garin na Konduga.

Kawo yanzu mahukuntan yankin, da jami'an rundunar 'yan sanda, ba su kai ga fitar da wani bayani a hukumance game da harin ba. (Saminu Hassan)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China