An shawarci Gwamnatin Tarayya da ta gaggauta zuba jari a fannin fasaha done ta inganta kara shigar da fannin wajen inganta tattalin arzikin ta.
Wani kwararren masani a fannin fasaha Mista Adetolani Eko ya bayar da Shawarar a jawabinsa a taron baje koli na fasaha karo na biyu na shekarar 2018 da ya guduna a jahar Legas.
Taken taron shi ne "Samar da Ci Gaba A kan Fannin Fasaha" har ila yau, baje kolin ya tattaro matasan 'yan kasuwa hudu ba tare da yin la'akari da kudi da kuma hadaka ba don cimma burin su a fannin.
Eko a karshe ya yi nuni da cewa, Gwamnatin tana da wadatattun kudin da zata iya ciyar da fannin gaba fiye damu, sai dai ya yi nuni da cewa, akwai tsare-tsare da gwamnatin ta samar don ciyar da fanninin gaba, amma duk da haka akwai bukatar gwamnati ta kara mayar da hankali wajen inganta fannin domin har yanzu akwai gibi a fannin da ba a cike ba.(Leadership A Yau)