Zimbabwen dai na da jimillar kujerun wakilci 210. Ana kuma sa ran kammala bayyana sakamakon zaben shugaban kasar da ya gabata nan da ranar Asabar 4 ga watan nan na Agusta.
Shugaban hukumar zaben kasar ta ZEC Priscilla Chigumba, ta ce hukumarta za ta ci gaba da bayyana sakamakon zaben da zarar sun tattara alkaluma. (Saminu Hassan)