Wata sanarwar da tarayyar ta fitar jiya, ta ce bisa gayyatar gwamnati da hukumar zaben kasar, ta riga ta tura ayarin shirinta dake sa sanya ido kan harkokin zabe.
Sanarwar ta ce gudanar da sahihin zabe bisa tsarin demokradiyya da zaman lafiya a kasashe mambobinta abu ne mai muhimmanci wajen cimma manufofinta, da kuma daukacin burinta na tabbatar da samar da zaman lafiya da cigaba da dunkulewar nahiyar.
A watan da ya gabata ne AU ta tura jami'ai 5 masu zaman kansu, dake taimakawa wajen shirya zabe zuwa Zimbabwe, daga ranar 15 ga watan Yuni zuwa 8 ga watan nan domin bada taimako.
Haka zalika, ayarin shirinta dake sa ido kan zabuka mai mutane 14, da suka hada da manazarta 4 da masu sa ido kafin, yayin da kuma bayan zabe guda 10, sun isa Harare, babban birnin Zimbabwe a ranekun 3 da 5 ga watan nan da muke ciki. (Fa'iza Mustapha)