in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Jam'iyyun siyasar Zimbabwe sun kammala yakin neman zaben kasar dake tafe ranar Litinin
2018-07-29 16:32:05 cri
A jiya Asabar ne jam'iyyun siyasar kasar Zimbabwe suka kammala gangamin yakin neman zabensu a yayin da ake sa ran jefa kuri'un babban zaben kasar a Litinin mai zuwa.

Baki daya shugaban kasar Zimbabwe Emmerson Mnangagwa da babban mai kalubalantarsa Nelson Chamisa na jam'iyyar hadaka ta MDC, sun karkare gangamin yakin neman zaben ne a Harare babban birnin kasar.

Kundin tsarin mulkin kasar Zimbabwe ya ayyana cewa, wajibi ne a tsayar da yakin neman zaben kasar sa'o'i 24 gabanin fara jefa kuri'a a kasar.

Dukkannin shugabannin sun bukaci magoya bayansu da su fito don kada kuri'unsu domin lashe zaben na ranar Litinin.

Mnangagwa da Chamisa sun kuma bukaci magoya bayansu da su zauna lafiya domin samun nasarar gudanar da zaben cikin lumana.

Mnangagwa ya ce, baya ga ingantuwar tattalin arziki da yake da burin kawowa kasar, jam'iyyarsa ta lashi takobin tabbatar da farfado da martabar Zimbabwe a idanun duniya muddin aka zabe shi.

Shi kuwa Chamisa ya ce, idan har aka zabe shi, jam'iyyarsa za ta gaggauta daukar dukkan matakan da suka dace don sharewa al'ummar kasar kukansu da kuma gina kasar Zimbabwe ba tare da nuna wariya ba, da mutunta hakkin ma'aikatan kasar da kuma bunkasa cigaba tattalin arzikin kasar.(Ahmad Fagam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China