Da yake jawabi ga dubban magoya bayan jam'iyyar a Marondera, dake gabashin lardin Mashonaland, Mnangagwa ya ce jam'iyyar ZANU-PF girmanta ya wuce ta dinga neman takalar rikici da kananan jam'iyyun kasar.
Mnangagwa ya fara jawabin nasa ne da bayyanawa taron gangamin irin shirye shiryen da jam'iyyar mai mulkin ke kokarin aiwatarwa nan da shekaru 5 masu zuwa har ma fiye. Ya ce daga cikin shirye shiryen akwai gagarumin aikin samar da lantarki da aikin hakar ma'adinai.
Yace gwamnati zata bada fifiko wajen zamanantar da aikin gona domin tabbatar da ganin manoman kasar sun samar da kyakkyawar yabanya.
Mnangagwa yayi alkawarin sake daga martabar kasar Zimbabwe a harkokin kasa da kasa bayan da kasar ta shafe shekaru masu yawa a matsayin saniyar ware. (Ahmad)