Kwamshinan hukumar zaben kasar Qubani Moyo, ya ce an kada kuri'a lami lafiya a fadin kasar, kuma matsalolin zabe kalilan aka samu, inda ya ce za a fara kidaya kuri'un bayan kammala zaben da misalin karfe 7 na dare a jiya.
Ya ce ana sa ran fara samun sakamakon zaben majalisar dokokin kasar da na hukumomin yankunan da safiyar yau Talata, yayin da na shugaban kasa zai kai zuwa ranar 4 ga watan Augusta mai kamawa. (Fa'iza Mustapha)