in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kwamitin sulhu ya yi Allah wadai da harin ta'addancin da aka kai a Pakistan
2018-07-15 15:46:39 cri
Kwamitin sulhu na MDD ya yi Allah wadai da kakkausar murya kan harin ta'addancin da aka kai ranar Jumma'a a yankin kudu maso yammacin kasar Pakistan, harin da ya halaka mutane 128 kana wasu 200 kuma suka jikkata.

Mambobin kwamitin sulhun wadanda suka bayyana hakan cikin wata sanarwa da aka rabawa manema labarai, sun kuma bayyana juyayi tare da mika sakonsu na ta'aziya ga gwamnatin Pakistan da iyalan wadanda harin ya rutsa da su, kana suka yi fatan samun sauki cikin hanzari ga wadanda suka jikkata.

Sun kuma yi kira da a hukunta wadanda suka kai harin, da masu shiryawa da ma wadanda ke daukar nauyin ayyukan ta'addanci. Sun kuma bukaci kasashe mambobin MDD da su hada kai sosai da gwamnatin Pakistan da sauran hukumomin da abin ya shafa a wannan fanni.

Harin kunar bakin waken da aka kai a Mastung dake kudu maso yammacin lardin Balochistan da aka shirya kaiwa wani taron kamfel din siyasa, shi ne hari mafi muni da aka kai a Pakistan a wannan shekara. (Ibrahim)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China