in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Ministan harkokin wajen Sin ya yi shawarwari tare da takwaransa na kasar Masar
2018-07-08 21:07:34 cri
Yau Lahadi, a birnin Beijing, memban majalisar gudanarwar kasar Sin, kana ministan harkokin wajen kasar, Wang Yi, ya yi shawarwari tare da takwaransa na kasar Masar, Sameh Hassan Shukry, wanda ya zo halartar taron ministoci karo na takwas na dandalin tattaunawa na hadin-gwiwar Sin da kasashen Larabawa. Wang Yi ya bayyana cewa, kasarsa na son karfafa mu'amala da cudanya tare da kasar Masar, kana, tana maraba da Masar don shiga ayyukan 'ziri daya da hanya daya', tare kuma da fadada hadin-gwiwa a fannonin da suka shafi masana'antu, da tattalin arziki, da cinikayya, da al'adu da tsaro da sauransu.

Sameh Hassan Shukry cewa ya yi, Masar ta yabawa muhimmiyar rawar da kasar Sin ta dade tana takawa wajen wanzar da zaman lafiya da kwanciyar hankali a yankin Gabas ta Tsakiya da kuma raya nahiyar Afirka. Masar na fatan hada gwiwa da kasar Sin bisa shawarar 'ziri daya da hanya daya' da ma tsarin dandalin tattaunawa na hadin-gwiwar Sin da kasashen Larabawa, da kuma fadada hadin-gwiwar a karkashin dandalin FOCAC, wato dandalin tattaunawa na hadin-gwiwar Sin da Afirka.(Murtala Zhang)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China