in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Wang Yi: Sin na fatan a kawar da makaman nukiliya a zirin Koriya
2018-06-12 14:56:20 cri

Ministan harkokin waje na kasar Sin Mista Wang Yi ya bayyana a yau a nan birnin Beijing cewa, Sin na fatan shugabannin Koriya ta arewa da Amurka za su amince da juna su kawar da sabanin dake tsakanisnu don daukar matakin da ya dace tare da cimma matsaya daya wajen ganin kawar da makaman nukiliya a zirin Koriya. Su kuma yi kokarin bullo da matakan wanzar da zaman lafiya a zirin. Mista Wang ya kara da cewa, yana fatan bangarori masu ruwa da tsaki su yi kokari kan wannan lamarin, ya kuma jaddada cewa, kasar Sin za ta ci gaba da taka muhimmiyar rawa kan wannan batu. (Amina Xu)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China