in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
An yi ganawa tsakanin ministocin harkokin waje na Sin da Afirka ta Kudu
2018-06-05 10:19:51 cri

Ministan harkokin wajen kasar Sin Mista Wang Yi, ya yi shawarwari da takwararsa ta kasar Afrika ta Kudu madam Lindiwe Sisulu a jiya 4 ga wata a birnin Pretoria.

Yayin shawarwarin nasu, Mista Wang ya bayyana cewa, Afrika ta Kudu za ta shirya taron shugabannin BRICS a watan gobe, yayin da Sin za ta gudanar da taron koli na dandalin tattaunawar hadin gwiwar a tsakaninta da kasashen Afrika a watan Satumban bana. Don haka ya kamata bangarorin biyu su yi amfani da wannan zarafi mai kyau, wajen nuna goyon baya ga juna, da kara yin hadin gwiwa tsakaninsu, ta yadda za su hadde tsare-tsarensu baki daya don cimma nasarar tarurrukan biyu.

Mista Wang ya kara da cewa, dangantakar abota bisa manyan tsare-tsare dake tsakanin Sin da Afrika ta Kudu, ba ma kawai na kawo amfani ga bangarorin biyu ba ne, har ma tana kara yin tasiri sosai ga kasashen duniya. Ya ce Sin na maraba da Afrika ta Kudu, ta halarci bikin baje koli na shige da fice karo na farko da Sin za ta gudana a watan Nuwamba mai zuwa a birnin Shanghai, kuma ta mai da hankali sosai kan sabbin shawarwarin da shugaba Matamela Cyril Ramaphosa ya gabatar, game da zuba jari. Kasar Sin tana mai fatan karawa kamfanonin Sin kwarin gwiwar shiga taron kolin zuba jari, da samar da guraben aikin yi a Afrika ta Kudu.

A nata bangare kuma, Madam Sisulu ta nuna cewa, Afrika ta Kudu na dora babban muhimmanci kan dangantakar dake tsakanin kasashen biyu daga dukkan fannoni. Kuma kasarta na matukar sa ran halartar shugaba Xi Jinping, taron koli na BRICS, da ziyararsa a Afrika ta Kudu. Wannan ne zai zamo karo na farko da shugaba Matamela Cyril Ramaphosa zai karbi shugaban wata kasa. Kuma ta kara da cewa, Afirka ta Kudu na godiya sosai ga goyon bayan da Sin take baiwa kasarta, wajen dauka nauyin shirya taron BRICS na wannan karo. Ban da wannan kuma, kasarta na nacewa ga manufar kasar Sin daya tilo a duniya, za kuma ta ci gaba da ingantawa, tare da bunkasa dangantakar hadin kai tsakanin kasashen biyu. (Amina Xu)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China