Shugaban kasar Sin Xi Jinping, da shugaban kasar Afirka ta kudu Cyril Ramaphosa, da shugaban kasar Rasha Vladimir Putin, da firaministan kasar India Narendra Modi sun halarci taron.
Shugabannin dake halartar taron sun jinjinawa jerin nasarorin da aka samu wajen hadin kan BRICS a cikin shekaru 10 da suka gabata, bisa tsarin tattaunawar koli ta BRICS, sun kuma ba da shawarwari kan hadin kai na nan gaba a tsakanin kasashen kungiyar, kana gaba daya suka amince da kafa wata makomar neman wadata tare da ta kunshi kowa da kowa.
A yayin jawabinsa, shugaban kasar Sin Jinping ya bayyana cewa, shekaru 10 masu zuwa, muhimmin mataki ne ga kasashen BRICS wajen neman ci gaba, da kuma fuskantar babbar dama da kalubale. Don haka ya kamata kasashen BRICS su yi aiki tukuru, wajen bude zango na biyu na "Shekaru 10 masu alfanu". (Bilkisu)