in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Hukumomin ciniki na Afrika ta kudu sun amince da manufofin BRICS na adawa da kafa shinge a kasuwanci
2018-07-29 16:40:06 cri

Hukumomin cinikayya sun bayyana goyon bayansu ga matakin da kungiyar kasuwanci ta BRICS ta amince da shi na kalubalantar sanya shinge a tsarin cinikayya da kuma amincewa da dokokin cinikayya na gamayyar kasashen duniya.

Wannan ya biyo bayan taron tattaunawar koli da aka gudanar ne na jami'an gwamnatocin kasashen duniya da jami'an masana'antu a birnin Johannesburg.

Babban jami'in sashen kula da al'amurran ciniki da masana'antu na Afrika ta kudu Yunus Hoosen ya jaddada, kamata ya yi a yi watsi da tsarin sanya shinge a harkokin cinikayyar.

Ya kara da cewa, a shekaru 16 da suka gabata akwai sauye-sauye game da tsarin cinikayyar duniya daga shiyyar arewaci zuwa kudanci. A halin yanzu BRICS ta kasance a matsayin wani tsarin hadin gwiwa dake yunkurin tabbatar da kyautata alakar abokantaka tsakanin kasashen duniya ta hanyar yin kiran neman a hada gwiwa tare don gina kyakkyawar makoma ga duniya.

Taron wanda ya samu halartar manyan jami'an gwamnatoci da na diplomasiyyar kasashen duniya da suka hada da kasashen Rasha, Indiya Afrika ta kudu, Indonesiya, Malasiya da Syria.

Shugaban majalisar ciniki da masana'antun Afrika ta kudu (SACCI) Zeph Ndlovu ya bayyana cewa, samar da tsarin gamayyar ciniki na kasashen duniya da bude kofa a sha'anin cinikayya su ne hanyoyin da za su kai ga nasara.

Da yake jawabi ga mahalarta taron, ya ce ba za su taba lamintar tsarin yin ciniki na falan daya da kuma sanya shinge a tsarin cinikayyar ba.

Ndlovu ya ce suna mutunta tsarin bude kofa ga sha'anin cinikayya wanda ya yi daidai da ka'idojin MDD.(Ahmad Fagam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China