in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Afrika ta kudu ta jinjinawa nasarar taron BRICS
2018-07-28 16:44:16 cri
Gwamnatin kasar Afrika ta kudu ta bayyana taron koli karo na 10, na kungiyar BRICS ta kasashen da za su zama jagara a fannin karfin tattalin arziki da suka hada da Brazil da Rasha da Indiya da Sin da Afrika ta Kudu da aka kammala a jiya Juma'a, a matsayin wanda ya cimma nasara.
Taron ya samu halartar shugabannin kasashen BRICS da wakilan cinikayya da na wasu kasashe da suka hada da Togo da Rwanda.
Shugaban Afrika ta Kudu Cyril Ramaphosa, ya shaidawa manema labarai cewa, taron ba wai na shan shayi ba ne, ya na mai cewa taro ne na tattaunawa tsakanin kasashe 5 da ke son ganin manufofi a aikace, inda ya ce kasashen, za su yi aiki tare don jagorantar zamani na 4 na sauya ayyukan masana'antu.
Shugaba Ramaphosa, ya ce Afrika ta Kudu ta wakilci nahiyar Afrika a wajen taron, inda take amfani da hanyoyi daban-daban na ganin taron ya zama dama ta samun ci gaba na bai daya a nahiyar. (Fa'iza Mustapha)
Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China