Mutane biyu da suka jikkata ranar Asabar da ta gabata sanadiyyar fashewar wani abu a wajen gangamin zabe a Bulawayo na Zimbabwe, sun mutu.
Karamar Minista mai kula da yankin Bulawayo Angeline Masuku, da ta tabbatar da mutuwar a jiya, ta ce mutanen biyu sun mutu ne sanadiyyar fashewar wani abu jim kadan bayan Shugaban kasar Emmerson Mnangagwa ya kammala jawabi ga gangamin.
Shugaba Mnangagwa ya tsira ba tare da kwarzane ba, duk da cewa mataimakinsa Kembo Mohadi da wasu 48 sun samu raunuka.
Tuni Mnangagwa ya bayyana harin a matsayin na tsoro daga makiyayansa, inda ya lashi takobin za a gudanar da babban zaben kasar a ranar 30 ga watan Yulin kamar yadda aka shirya. (Fa'iza Mustapha)