A jiya Lahadi ne mataimakin shugaban kasar Constantino Chiwenga, ya shaida wa mahalarta gangamin yakin neman zaben da tsagin shugaban kasar mai ci ke gudanarwa a Chitungwiza dake kudancin birnin Harare, cewar harin da wani abun fashewa da aka kai wa shugaban, yayin da yake sauka daga dandamalin da ya gabatar da jawabi a Bulawayo, aiki ne na ta'addanci. (Saminu Hassan)