in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Mnangagwa ya yi Allah wadai da yunkurin hallaka shi, ya nanata ci gaba da yakin neman zabe
2018-06-24 16:24:01 cri

Shugaban kasar Zimbabwe Emmerson Mnangagwa ya ce an kaddamar da hari ne da nufin ganin bayansa a lokacin da yake gangamin yakin neman zabe a Bulawayo wanda ya bayyana harin da cewa na matsorata ne kuma ko kadan ba zai yi kasa a gwiwa ba wajen ci gaba da yakin neman zaben shugaban kasar wanda za'a gudanar a ranar 30 ga watan Yuli.

A sakon da ya wallafa ta shafinsa na Facebook a daren ranar Asabar, Mnangagwa ya bukaci jama'ar kasar Zimbabwe da su zama tsintsiya madaurinki daya kuma su hada kai wajen kawar da banbancin ra'ayin siyasa a tsakaninsu cikin lumana.

Ya ce da yammacin jiya Asabar, a lokacin da suke barin yankin Bulawayo a wani gangami mai ban mamaki, sai kawai aka samu fashewar wani abu. Fashewar ta jikkata mutane da dama, kuma tuni ya ziyarce su a asibiti domin duba halin da suke ciki. A yayin da suke dakon karin bayani, shugaban ya ce, yana addu'a ga dukkan wadanda wannan harin na rashin tunani ya shafa.

Ya ce sun gudanar da gangamin yakin neman zaben cikin yanayi mai kyau da kwanciyar hankali, kuma ba za su taba lamunta a sake kaddamar da makamancin wannan hari na matsorata ba a yayin da ake gaf da gudanar da zabukan kasar.

Mnangagwa wanda ya tsira ba tare da samun koda kwarzane ba, kuma an garzaya da shugaban daga filin taron cikin nasara bayan kaddamar da harin na ranar Asabar wanda ya jikkata mutane da dama.

A cewar kafar yada labaran kasar ta ZBC, an rawaito mataimakin shugaban kasar Kembo Mohadi ya samu raunuka a kafarsa kuma tuni aka garzaya da shi zuwa asibin kasar domin ba shi magani. (Ahmad Fagam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China