in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
An bude taron kolin shugabannin kasashen BRICS karo na 10
2018-07-27 11:14:49 cri

Jiya Alhamis ne a birnin Johannesburg na Afrika ta kudu, aka bude taron kolin shugabannin kasashen BRICS karo na 10. Shugaban kasar Afrika ta kudu Cyril Ramaphosa shi ne ya jagoranci taron, wanda ya samu halartar shugaban Sin Xi Jinping, na Brazil Michel Temer, na Rasha Vladimir Putin, da firaministan kasar Indiya Narendra Modi. Yayin ganawar, shugaba Xi ya nuna cewa, ya kamata kasashen BRICS su yi amfani da wannan zarafi mai kyau don zurfafa dangantakar abota bisa manyan tsare-tsare tsakaninsu, da inganta hadin kai ta fuskoki uku wato tattalin arziki, siyasa da al'adu, ta yadda za a kai ga bude wani sabon babi na hadin kai a tsakaninsu a cikin shekaru 10 masu zuwa.(Amina Xu)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China