Taron wanda ya kunshi tawagogin wakilan kasashen Afrika kimanin 38 kan shirin na CWC da wasu wakilai daga kungiyoyin kasa da kasa da na shiyya-shiyya.
Taron, wanda aka shirya tare da hadin gwiwar sakatariyar kungiyar hana yaduwar makamai masu guba ta kasa da kasa wato (OPCW), zai mayar da hankali ne game da irin rawar da gwamnatocin kasashen Afrika za su taka game da aiwatar da shirin na CWC, da kuma yadda za su tafiyar da shirin wajen aiwatar da yarjejeniyar da aka cimma a matakai na kasashen.
Taron an shirya shi ne da nufin tabo muhimman batutuwa wadanda kasashen na Afrika za su baiwa fifiko, da kuma sake tsara hanyoyin da za'a kara yin hadin gwiwa tsakanin kwamitin gudanarwar OPCW da na kasashen Afrika. (Ahmad Fagam)