A yayin ziyararsa a kasar ta Morocco, ana sa ran shugaba Buhari ya tattauna da sarki Mohammed na 6, sannan su jagoranci bikin sanya hannu kan wasu jerin yarjejeniyoyi, kamar yadda wata sanarwa da mahukuntan kasar suka fitar.
Dangantaka tsakanin Najeriya da Morocco dai ta ci gaba da bunkasa a 'yan shekarun da suka gabata. Koda a ziyarar da sarkin na Morocco ya kai Najeriya a watan Disamban shekarar 2016, kasashen biyu sun sanya hannu kan wasu yarjejeniyoyi, tare da cimma matsaya game da hadin gwiwa a aikin shimfida bututun iskar gas, matakin da zai kai ga hade kasashen arewaci da yammacin nahiyar Afirka da kuma baiwa shiyyar damar cin gajiyar makamashi na kashin kanta, da hanzarta aiwatar da ayyukan samar da wutar lantaki da bunkasa muhimman ayyukan da suka shafi harkokin tattalin arziki da masana'antu. (Ibrahim Yaya)