Shugaban wanda ya bayyana hakan cikin wata makala da ya rubuta game da taron kolin shugabannin kungiyar BRICS karo da za a gudanar a birnin Xianmen dake nan kasar Sin daga ranar 3 zuwa 5 ga watan Satumba, ya ce ya yaba da gagarumar gudummawar da kasar Sin ta bayar a matsayinta na mai rike da shugabancin kungiyar na wannan shekara.
Putin ya ce, gudummawar da kasar ta Sin ta bayar, ya baiwa kasashen kungiyar damar kara samun ci gaba a dukkan manyan fannonin hadin gwiwar dake tsakaninsu, ciki har da siyasa da tallalin arziki da kuma al'adu. (Ibrahim)