Ya ce yana da tabbacin cewa, duniya za ta ci gaba da mutunta MDD, a matsayin muhimmiyar kafa da ke goyon bayan zaman lafiya da tsaro a duniya baki daya, kana jigon neman ci gaba da kare hakkin bil-Adam.
Jami'in na MDD ya kuma jaddada cewa, duniya ba za ta kasance ba tare da tsarin wanzuwar bangarorin daban-daban da kuma dokokin alakar kasa da kasa da aka kafa ba. Ya ce hakan ba ya nufin, ba za a aiwatar da gyare-gyare a MDD ba. Amma kamata ya yi a gudanar da gyare-gyaren da za su karfafa tare da yin tasiri wajen magance bukatu da burin da ake fatan cimmawa a MDD.
Guterres na wadannan kalamai ne kan tambayar da aka masa game da takalar da ta kunno kai, musamman daga Washington kan dokar da aka bullo da ita bayan yakin duniya na biyu, wanda MDD na da hannu a ciki. (Ibrahim)