Haka kuma ya ce, tun lokacin da aka kafa tawagar wakilan kasar Sin dake kungiyar AU, ana ci gaba da karfafa hadin gwiwar a tsakanin Sin da Afirka, kuma tawagar wakilan Sin ta ba da babban taimako ga kungiyar AU wajen kafa yankin ciniki cikin 'yanci na nahiyar Afirka, da zirga zirgar mutane na mambobin kungiyar AU cikin 'yanci, da kuma kafuwar kasuwar sufurin jiragen sama ta Afrika da dai sauransu.
A nasa bangaren, jakada Kuang Weilin ya nuna cewa, cikin shekaru uku da suka gabata, an zurfafa huldar dake tsakanin kasar Sin da kungiyar AU, kuma hadin gwiwar dake tsakanin bangarorin biyu ya sami babban ci gaba a fannonin ma'amalar dake tsakanin shugabanninsu, gina ababen more rayuwa, kiwon lafiya da kuma kiyaye zaman lafiya da dai sauransu.
An bude ofishin tawagar wakilan kasar Sin dake kungiyar AU ne a watan Mayun shekarar 2015, kuma jakada Kuang Weilin shi ne shugaba na farko na wannan tawaga. (Maryam)