in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Yankin arewacin Afrika ne ya fi aiwatar da muradun ci gaba masu dorewa
2018-06-20 10:12:36 cri
Wani sabon rahoto da Tarayyar Afrika AU ta fitar jiya a hedkwatarta dake Addis Ababa na Habasha, ya ce yankin Arewacin Afrika ne ya fi kowane aiwatar da muradun ci gaba masu dorewa da ake son cimmawa zuwa shekarar 2030.

Cibiyar tabbatar da muradun na nahiyar Afrika ne ya fitar da rahoton da aka yi wa lakabi da The Africa SDG Index Dashboards 2018, da ya kunshi kasashe 51.

Daga cikin yankuna 5 na nahiyar, yankin arewaci ne ke kan gaba, yayin da yankin Afrika ta tsakiya ya kasance koma baya, inda yake bi wa yankin gabashin nahiyar.

A cewar rahoton, daga cikin kasashe 5 dake kan gaba a Afrika, Morocco ce ta 1, wadda ke kan hanyar cimma muradun da kaso 66.1.

Da take gabatar da rahoton, jami'ar cibiyar Lina Henao, ta ce duk da an fi yin kokari kan muradi na 13 mai batun sauyin yanayi, rahoton ya bayyana cewa, galibin kasashen Afrika sun fi rashin tabuka abun kirki a muradun dake da alaka da kayakin more rayuwa da kiwon lafiya da fannin shari'a, bayan fannin aikin gona da na wadatar abinci da makamashi.

Ta ce kaso 70 na kasashen ba su yi wani kokari a bangaren aikin noma da na wadatar abinci da makamashi ba, sai dai duk da haka, ya fi wanda suka yi a bangaren samar da kayayyakin more rayuwa da kiwon lafiya da harkokin shari'a.

Darakta Janar na cibiyar Belay Begashaw, ya shaidawa Xinhua cewa, har yanzu da sauran tafiya ga kasashe da dama wajen cimma muradun. (Fa'iza Mustapha)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China