Faki ya fada a lokacin tattaunawa da firaiministan Somaliya, Hassan Ali Khaire, a helkwatar kungiyar tarayyar Afrika dake Addis Ababa babban birnin kasar Habasha, ya ce tsoma bakin yana yin barazana ga zaman lafiyar da ake ginawa da kuma kokarin da ake yi a halin yanzu na tabbatar da zaman lafiya a Somaliya.
Ya ce tsoma bakin wata babbar barazana ce dake mayar da hannun agogo baya a kokarin da ake na hadin gwiwa tsakanin (AMISOM) da dakarun tsaron kasar Somaliya, inda ya bukaci dukkan masu shiga tsakani na kasashen waje da su guji yin dukkan abubuwan da za su wargaza shirin zaman lafiyar Somaliya.
Sanarwar ta ce, shugabannin biyu sun tattauna game da irin ci gaban da aka samu a halin yanzu bayan da gwamnatin Somaliya ta aiwatar da ajandar sauye sauye a harkokin siyasa, tattalin arziki da tsaron kasar. (Ahmad Fagam)