Wang Yi ya bayyana haka ne lokacin da yake amsa tambayoyi, yayin wani taron manema labarai na hadin gwiwa da ya yi da takwaransa na Austria, Karin Knessl.
Taron wanda zai gudana yau Juma'a a Vienna, da zai kunshi Ministocin harkokin wajen Faransa da Jamus da Rasha da Birtaniya da Iran da Columbia da Sin, shi ne irinsa na farko da za a yi tsakanin bangarorin da suka rage cikin yarjejeniyar Nukiliya Iran, tun bayan janyewar Amurka.
A cewar Wang Yi, gazawa wajen ci gaba da aiwatar da yarjejeniyar, ba batun Nukiliya Iran kadai za ta yi wa illa ba, ya na mai cewa, za ta yi mummunan tasiri kan lokacin da ake ciki na son kawar da makaman nukiliya da kuma yanayin yankin gabas ta tsakiya.
Ministan da ya bayyana taron na yau a matsayin wanda ake bukata kuma ya zo a kan gaba, ya ce a shirye kasar Sin ta ke ta yi aiki da bangaren Turai, wajen ci gaba da yin dukkan mai yiwuwa don ganin an aiwatar da yarjejeniyar. (Fa'iza Mustapha)