in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Ministan harkokin wajen kasar Sin ya bayyana ra'ayin kasar dangane da batun nukiliyar Iran
2018-07-07 16:25:25 cri
Mamban majalisar gudanarwar kasar Sin, kana ministan harkokin wajen kasar, mista Wang Yi, ya halarci taro kan batun nukiliyar Iran, wanda ministocin harkokin wajen kasashen dake cikin yarjejeniyar suka yi jiya Juma'a a birnin Vienna na kasar Austria.

Yayin ganawarsa da manema labaru bayan taron, mista Wang Yi, ya ce, taron yana da muhimmanci, kana ya zo a kan gaba, wato a daidai lokacin da yarjejeniyar nukiliyar ta Iran ke fuskantar babban kalubale. A cewar jami'in na kasar Sin, mahalarta taron sun cimma ra'ayi daya wajen zartas da wata hadaddiyar sanarwa ta musamman, wadda ta nuna niyyar kasashen, ta ci gaba da aiwatar da yarjejeniyar nukiliyar, da kin yarda da daukar matakin sanya takunkumi bisa ra'ayi na radin kai, da kuma kokarin kare tsarin hana bazuwar makaman nukiliya a duniya.

Bugu da kari, Wang Yi ya ce ra'ayin kasar Sin dangane da batun nukiliya na kasar Iran shi ne: da farko, ya kamata a bi ka'idojin kasa da kasa; na biyu shi ne, a aiwatar da yarjejeniyar da aka kulla. Sa'an nan na uku, a yi kokarin tabbatar da kwanciyar hankali a yankin gabas ta tsakiya; kana na hudu shi ne, a yi watsi da dabarar daukar mataki na kashin kai. Na biyar kuma, a tsaya kan manufar daidaita sabanin ra'ayi ta hanyar tattaunawa da shawarwari. (Bello Wang)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China