Shugaban kasar Iran Hassan Rouhani, ya sanar a jiya Laraba a birnin Vienna, cewar babu wani bangare da zai amfana daga janyewar da kasar Amurka ta yi daga yarjejeniyar makaman nukiliyar kasar Iran.
Ya ce "Ko ita kanta Amurka, ko wata kasa ta daban babu wadda za ta amfana daga janyewar yarjejeniyar makaman nukiliyar kasar Iran".
Ya fadawa taron manema labarai cewa, Iran ta amince da cigaba da bayar da hadin kai game da yarjejeniyar, kuma za ta sauke nauyin dake wuyanta, idan har sauran bangarorin da abin ya shafa sun kiyaye moriyar kasar. (Ahmad Fagam)