in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Majalisar dokokin Sudan ta kudu ta amince da tsawaita wa'adin mulkin shugaba Salva Kiir
2018-07-13 13:13:18 cri
Shugaban majalisar dokokin kasar Sudan ta kudu Anthony Makana ya sanar a jiya Alhamis cewa, majalisar ta jefa kuri'u inda ta amince da tsawaita wa'adin mulkin shugaban kasar mai ci Salva Kiir zuwa shekarar 2021, wato shekaru 3 ke nan. Bayanai na cewa, wa'adin gwamnati mai ci zai kare ne a watan Yuli, amma an tsawaita wa'adin mulkin shugaba ne domin magance matsalar gibin shugabanci.

Kasar Sudan ta kudu ta samu 'yancin kai ne a shekarar 2011, kuma Salva Kiir shi ne shugaban kasar na farko. Da ma kasar ta shirya gudanar da zaben shugaban kasa a watan Yulin shekarar 2015, amma sakamakon tashin hankalin da kasar take fuskanta, ya sa majalisar dokokin kasar ta amince ta tsawaita wa'adin mulkin shugaba Salva Kiir zuwa watan yulin bana. (Bilkisu)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China