Cikin wata sanarwa da mataimakin shugaban kasar na farko Taban Deng Gai ya karanta a jejiberin bikin ranar cikar kasar 7 da samun 'yancin kai, shugaba Kiir ya ce, dakarun gwamnati da na 'yan adawa sun cimma yarjejeniyar tsagaita bude wuta, kuma yana fatan yarjejeniyar za ta kai ga dorewa.
A ranar jumma'ar da ta gabata ce, gwamnatin kasar ta soke shirye-shiryen bikin samun 'yancin kasar karo na uku a jere saboda abin da ake kira matsalar kudi da jeririyar kasar take fuskanta.
A halin da ake ciki kuma, a ranar Jumma'ar ce bangarorin kasar suka sanya hannu kan yarjejeniyar tsaro na wucin gadi a Khartoum na kasar Sudan, ta yadda za a samu nasarar girka matakan tsaro a lokacin mika mulki.
Yanzu haka dai shugaba Kiir na Kampala na kasar Uganda, inda yake wata ziyarar tabbatar da zaman lafiya, a kokarin da kasashen dake shiyyar ke yi na kawo karshen rikicin da kasar take fuskanta. (Ibrahim)