in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Zumuncin da ke tsakanin Sin da Afirka
2018-07-25 15:59:54 cri

Sin da Afirka suna da nisan kilomita fiye da dubu 10 a tsakaninsu, amma suna da alaka da juna ta hanyar sada zumunta a tsakaninsu da raya kokarin cimma buri daya. Ganawa a tsakanin manyan shugabannin bangarorin biyu ya shaida zumunta mai zurfi dake tsakaninsu. A halin yanzu, shugaban kasar Sin Xi Jinping yana ziyara a kasar Afirka ta Kudu, kafin haka, ya kai ziyara kasashen Senegal da Ruwanda, kuma wannan shi ne karo na 4 da shugaban ya kai ziyara nahiyar Afrika a cikin shekaru 5 da suka gabata.

Shugabannin kasashen Afirka ma su sha kawo ziyara kasar Sin. Kafin karshen watan Maris na bana bayan kammala manyan taruruka biyu na kasar Sin, shugabannin kasashen Afirka da suka hada da Kamaru da Namibia da Zimbabwe sun kawo ziyara kasar Sin bi da bi. Hakan ya sa bana ta zama tamkar shekarar Afirka a fannin diplomasiyya ga kasar Sin. A watan Satumba na bana kuma, za a gudanar da taron koli na dandalin tattaunawar hadin gwiwar Sin da Afirka a birnin Beijing, inda shugabannin Sin da na kasashen Afirka fiye da 50 za su tsara shirin raya kasashen Afirka bisa shawarar "ziri daya da hanya daya", don kara sada zumunta da neman ci gaba a kasar Sin da kasashen Afirka.

Sin da Afirka na da daddaden zumunci, tun lokacin da al'ummomin Sin da Afirka suka yi gwagwarmayar neman 'yancin kansu, suka fara taimakawa juna da kuma goyon bayan juna. Kana goyon bayan da kasashen Afirka suka nuna wa kasar Sin kan manufar "kasar Sin daya tak" a duniya ya nuna zumuncin dake tsakaninsu sosai. Haka kuma, kasar Sin ita ma ta ci gaba da taimakawa kasashen Afirka wajen neman bunkasuwa a dandalin duniya.

Tun daga shekarar 1990, ministan harkokin wajen kasar Sin ya kan ziyarci kasashen Afirka a farkon ko wace shekara. Wannan al'adar da Sin ta kiyaye cikin kusan shekaru 30 da suka gabata, ta shaida taimako da goyon baya dake tsakanin Sin da Afirka.

Manufar zumunta dake tsakanin Sin da Afirka ita ce "cimma moriyar juna bisa adalci" da kuma "neman ci gaba tare". Taron dandalin tattaunawar hadin gwiwa tsakanin Sin da Afirka ya nuna "adalci" da "hadin gwiwa" a huldar dake tsakanin bangarorin biyu. Kuma kasar Sin tana taimaka wa kasashen Afirka ba tare da wani sharadi ba, lamarin da ya nuna mutuntawa ga kasashen Afirka. Kana, kasar Sin ta ci gaba da bude kasuwanninta ga kasashen Afirka, da taimakawa kasashen Afirka kan harkokin gina muhimman ababen more rayuwa, shimfida hanyoyi, gina yankin masana'antu da dai sauransu, dukkansu sun nuna ka'idar "neman ci gaba cikin hadin gwiwa" sosai.

Sin da Afrika su kan marawa juna baya yayin da suke fuskantar mawuyacin hali. Dangantakar dake tsakaninsu tamkar aminai ne, samun moriya tare abu ne mai sauki, amma marawa juna baya a yanayi mai wahalar gaske zai iya bayyana sahihin zumuncin. Al'ummar Sinawa ba za su manta da tallafin da kasashen Afrika suka ba su ba, yayin akuwar bala'in girgizar kasa na Wen Chuan na watan Mayu na shekarar 2008 da makamancin wannan bala'in da ya auku a Yushu a watan Afrilu na shekarar 2010, duk da cewar ba su da wadata sosai, Alal misali, Equatorial Guinea wadda ba ta da wadata kuma yawan al'ummar miliyan 1 ne kawai, ta samar da tallafin kudi har Euro miliyan 1, wannan daidai yake da tallafin Euro 1 ga ko wane dan kasar ya baiwa kasar Sin.

A sa'i daya kuma, jama'ar Afrika ba za su manta cewa, Sin ba ta yi wata-wata ba wajen baiwa kasashen Afrika tallafi da taimako yayin da suka yi fama da talauci da annobar cututtuka. Alal misali a yanayin zafi na shekarar 2011, wasu kasashen dake arewa maso gabashin nahiyar Afrika ciki hadda Somaliya sun yi fama da bala'in fari, Sin ta ba su tallafin hatsi da kudi sau biyu cikin lokaci, da darajarsu ta kai dala RMB miliyan 443.2.

Bayan barkewar cutar Ebola a wasu kasashen dake yammacin nahiyar Afirka kamar Guinea da Liberiya da Saliyo a watan Maris na shekarar 2014, gwamnatin kasar Sin ta ba su taimakon kayayyaki da kudade har sau hudu, gaba daya darajarsu ta kai kudin Sin yuan miliyan 750, kana tawagogin likitocin da kasar Sin ta tura a wuraren dake fama da barkewar cututtuka ba su janye ba, inda suka ci gaba da gudanar da aikin ceton jama'a, domin dakile wannan matsala tare da aminansu na kasashen Afirka. Alkaluman na nuna cewa, adadin likitocin kasar Sin dake aiki a wuraren da aka samu barkewar cutar Ebola a shekarar 2014 ya zarta 700, a don haka ministan harkokin wajen kasar ta Saliyo ya yaba da taimakon da kasar Sin ta samar wa kasashen Afirka matuka, inda ya bayyana cewa, kasar Sin sahihiyar aminiyar su ce.

Zumuncin dake tsakanin kasar Sin da kasashen Afirka yana karuwa sannu a hankali tun bayan kokarin da sassan biyu suka yi, kawo yanzu hadin gwiwar dake tsakaninsu ya shiga wani sabon matsayi yayin da kasashen Afirka suke kokarin aiwatar da tsarin raya kasa bisa shawarar ziri daya da hanya daya. Duk da cewa duniya na fuskantar manyan sauye-sauye a halin yanzu, haka kuma wasu kasashe suna mai da hankali kan muradun kansu kawai, ko kuwa wasu suna ba kariya ga harkokin cinikayarsu, ya zama dole a kara darajanta zumuncin dake tsakanin Sin da Afirka saboda yana da muhimmanci matuka ga sassan biyu. (Zainab, Maryam, Amina, Jamila)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China