Kasar Sin ta bukaci a kawo karshen duk wasu munanan kalamai game da dangantakar dake tsakanin Sin da Afrika.
Mataimakin ministan harkokin wajen kasar Sin Chen Xiaodong, ya yi wannan kira ne a lokacin bude taron dandalin kwararrun masanan Sin da Afrika karo na 7.
Manufofin kasar Sin game da Afrika na gaskiya ne kuma yana samar da sakamako mai gamsarwa, in ji Chen.
Mista Chen ya ce, hadin gwiwar babu wani batu na siyasa a cikinsa, batu ne na bunkasa tattalin arziki da zamantakewar al'ummar Afrika, da nufin cin moriyar juna ta fuskar tattalin arziki.
Kasar Sin tana daukar batutuwan cigaban Afrika da matukar muhimmanci, tana samar da kudade da kuma zuba jari a bisa hanyoyi mafi dacewa, kuma tana kokarin shawo kan duk wata barazanar da ake iya fuskanta, inji Chen.(Ahmad Fagam)