A gun taron, wakiliyar musamman ta kasar Sin mai kula da harkokin Afirka Xu Jinghu ta bayyana cewa, Sin da kasashen Afirka suna da buri iri daya, suna kuma yin koyi da juna kan akidar raya kasa, da samun nasarori kan hadin gwiwar su a fannoni daban daban, wanda hakan ya samar da gudummawa ga kasashen Afirka, wajen neman samun bunkasuwa da kansu.
A nasa bangare, zaunannen wakilin kungiyar AU dake ofishin MDD na Geneva Ajay Kumar Bramdeo, cikin jawabin da ya gabatar a gun taron, ya godewa kasar Sin, bisa kira da ta yi, da a gudanar da wannan taro. Ya kuma bayyana fatansa na ganin yadda Afirka ta kara zurfafa hadin gwiwa tare da kasar Sin, a fannonin samun bunkasuwa, da tabbatar da hakkin dan Adam da sauransu, a kokarin kawo alheri ga jama'ar kasashen Afirka.
Su kuwa wakilan kasashen Togo, Masar, Afirka ta Kudu, Gabon da sauransu dake ofishin MDD na Geneva, nuna yabo suka yi ga Sin, da da ta kira taron tare da kasashen Afirka. A ganinsu taron na da babbar ma'ana wajen jaddada hakkin samun bunkasuwa, da tabbatar da bin ra'ayin kasancewar bangarori da yawa, da raya ayyukan hukumar kare hakkin dan Adam ta MDD, da kuma sa kaimi ga tabbatar da hakkin dan Adam. (Zainab)