in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
An rufe taron kolin tattaunawa tsakanin CPC da jam'iyyun siyasa na Afirka
2018-07-19 11:20:19 cri

Jiya Laraba ranar 18 ga wata bisa agogon wurin, aka rufe taron kolin tattaunawa tsakanin Jam'iyyar Kwaminis ta kasar Sin wato CPC da jam'iyyun siyasa na kasashen Afirka a kasar Tanzaniya. Taron da ya samu kyakkyawan sakamako bisa hadin gwiwar jam'iyyar CPC da jam'iyyun siyasa na kasashen Afirka.

A ranar 18 ga wata bisa agogon wurin, aka rufe taron koli na yini biyu na tattaunawa tsakanin Jam'iyyar Kwaminis ta kasar Sin wato CPC da jam'iyyun siyasa na kasashen Afirka a Dar es Salaam na kasar Tanzaniya. Xu Lvping, mataimakin ministan hukumar huldar kasa da kasa ta kwamitin tsakiya na Jam'iyyar CPC ya bayyana a gun bikin rufe taron, cewar an cimma ra'ayi bai daya kan batun koyi da juna, a tsakanin jam'iyyar CPC da jam'iyyun siyasa na Afirka, a kokarin raya makomar Sin da Afirka bisa hadin kai.

A cikin wadannan kwanaki biyu, wakilan jam'iyyar CPC da na wasu jam'iyyun siyasa kimanin 40 daga kasashen Afrika kusan 40, da ma wakilan kungiyoyin jam'iyyun siyasar Afirka, sun tattauna sosai kan batun neman samun hanyar ci gaban bisa halin da kasashe suke ciki.

Kasashen Afirka daban daban da suka halarci taron, sun jinjina wannan taron kolin sosai, inda babban daraktan Jam'iyyar Jubilee ta kasar Kenya Raphael Tuju ya furta cewa, taron ya samar wa jam'iyyar CPC, da jam'iyyun siyasa na Afirka wata kyakkyawar damar cudanyar juna, da koyi da juna.

"Wannan taron koli, ya samar da wata kyakkyawar damar tattaunawa ga jam'iyyun siyasa na kasashen Afirka, inda ake iya taimakawa juna bisa fifikon su. Haka kuma an kara fahimtar juna a tsakaninmu da Jam'iyyar CPC, da kara dankon zumuncin mu. Jam'iyyar CPC na da dimbin fasahohi wajen mulkin kasa, wadanda za su ba mu taimako wajen raya kasashenmu."

A nasa bangaren, Juilao Mateus Paulo, Darakta mai kula da harkokin waje na Jam'iyyar PMLA ta kasar Angola, wanda ke kan karagar mulkin kasar yana ganin cewa, taron kolin tattaunawar ya samar da wani kyakkyawan tsarin tattaunawa a tsakanin Sin da Afirka, kana yana fatan za a iya ci gaba da aiwatar da tsarin.

"A ganina, tsarin hadin gwiwa da cudanya a tsakanin Jam'iyyar CPC da jam'iyyun siyasa na Afirka na da kyau da babbar ma'ana. Ganin yadda Jam'iyyar PMLA ta kasance wata jam'iyyar da ta neman ci gaba na a zo a gani, muna fatan za a iya bunkasa yin irin wannan cudanya a tsakanin jam'iyyar CPC da jam'iyyun siyasa na Afirka, domin kawo alheri ga bunkasuwar jam'iyyun siyasar Afirka."

Yanzu kasashen Afirka na cikin zamanin samun bunkasuwa, yadda za a raya kasa yadda ya kamata wani batu ne da ya jawo hankulan kasashen Afirka sosai. Babban daraktan Jam'iyyar Chama cha Mapinduzi ta kasar Tanzaniya Bashiru Ali Kakurwa ya bayyana cewa, yanzu kasar Tanzaniya na aiwatar da shiri na biyu na shekaru biyar na raya kasa, tana fatan kara yin mu'amala tare da Sin kan fasahohin gudanar da harkokin kasa, domin kyautata kwarewar jam'iyyar a wannan fanni.

"Ya kamata a tsara ka'idojin biyayya a bayyane bisa adalci, wannan ne abin da muka koya daga Jam'iyyar CPC. Ban da haka, mun fahimci muhimmancin hadin kai, jama'ar Sin na da hadin kai sosai, jama'ar kasarmu ma hakan suke. Baya ga ma hadin gwiwa a tsakanin kasarmu da kasar Sin, akwai kuma cudanya sosai a tsakanin jam'iyyun kasashen namu."

Abin da ya fi burge Mr. Bashiru shi ne ra'ayin Jam'iyyar CPC kan batun yaki da cin hanci da rashawa, wanda ya samu babban yabo daga wajensa.

"Cin hanci ya yi kama da guba, wanda zai iya kawo babban cikas ga ci gaban kasa da zamantakewar al'umma. Sanin kowa ne, kasar Sin ba ta hakuri ko kadan kan batun cin hanci a gudanar da gwamnatinta da jam'iyyarta. Ina ganin cewa, Shugaba Xi Jinping ya yi namijin kokari wajen yaki da cin hanci da rashawa. A kasarmu ta Tanzaniya ma, Shugaba Magufuli shi ma yana kokari a wannan fanni. Muna kara kokari wajen koyon fasahohi masu nasaba da hakan."(Kande Gao)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China