Da yake bayyana hakan ga manema labarai a jiya Litinin, Mr. Sisulu ya jaddada muhimmancin aiwatar da manufofin tattalin arziki a bude, tare da baiwa dukkanin kasashe damar shiga a dama da su, a harkokin da suka jibanci dunkulewar duniya, kamar yadda hakan ke kunshe cikin sanarwar da zaman ministocin wajen kasashe masu samun bunkasar tattalin arziki na watan Yuni ya ayyana.
Taron BRICS dake tafe zai samu halartar shugabanni kasashe mambobin kungiyar da suka hada da Brazil, da Rasha, da India, da China da Afirka ta kudu, wadanda ake sa ran za su tattauna game da matakan tunkarar kalubalen da ke fuskantar duniya baki daya. (Saminu Hassan)