in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
An bukaci kasashen duniya su taimakawa nahiyar Afrika daidaita sauyin yanayi
2018-06-20 11:42:22 cri
An kaddamar da taron kasa da kasa karo na 5, kan daidaita sauyin yanayi, jiya a birnin Cape Town na Afrika ta kudu, inda mahalarta suka bukaci al'ummomin duniya su taimakawa nahiyar Afrika daidata matsalar sauyin yanayi.

Taron na yini 3, wanda ke gudana karon farko a nahiyar Afrika, ya hada jami'an gwamnati da masana kimiyya da kwararru da 'yan kasuwa sama da 1,000, wadanda suka fito daga sassa daban- daban na duniya, domin musayar ra'ayi da koyo da samar da dabarun daidaita sauyin yanayi.

Taron ya bayyana rauni da nahiyar Afrika ke da shi ta fuskar sauyin yanayi. Mahalarta sun kuma amince cewa, tasirin da dumamar yanayi ke yi ya yi yawa idan aka kwatanta da tasirinsa kan bil adama a lokaci mai tsawo da ya gabata.

Mataimakin Darakta Janar na sashen kula da muhalli na Afrika ta kudu Tlou Ramaru, ya ce babu makawa, magance kalubalen da ke tattare da sauyin yanayi na bukatar daidato, sai dai za a iya samun alaka sosai tsakanin yawan matakan daidaiton da kuma yawan illoli, da nasarori ko kuma gazawar kokarin rage fitar da hayaki mai guba.

Wani rahoton da kwararru suka fitar yayin taron ya nuna cewa, matsanancin yanayi, da ya hada da fari da ambaliyar ruwa da matsanancin zafi, ka iya karuwa da aukuwa a kai a kai musammam a Afrika. (Fa'iza Mustapha)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China