in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Jami'an Kasar Afrika ta kudu za su karbi horo kan yankunan kasuwanci na musammam a kasar Sin
2018-05-29 09:48:57 cri
Tawagar jami'ai 50 na kasar Afrika ta Kudu, dake da kwarewa kan harkokin yankunan raya tattalin arzki, za su karbi horo kan bangaren a kasar Sin, daga ranar 31 ga wannan watan zuwa 7 ga watan Yuni.

Jami'an na ofisoshin larduna da kananan hukumomi da ma'aikatu, na ma'aikatar ciniki da masana'antu ta Afrika ta kudu, dake da alhakin aiwatar da yankin raya tattalin arziki na musammam na kasar ne za su karbi horo kan fannin a Tianjin.

Mataimakin ministan ma'aikatar, Bulelani Magwanishe, ya ce manufar horon ita ce, samarwa jami'an ilimin yadda za su tsara da kula da rayawa da kuma gudanar da harkokin yankunan raya kasuwanci na musammam.

Gwamatin Afrika ta Kudu ta bayyana godiya ga gwamnatin kasar Sin, bisa damar da ta samar na karawa jami'anta ilimi da bayanai da dabarun gudanar da shirin yankunan raya tattalin arziki.

Bulelani Magwanishe, ya ce ya zama wajibi kasar ta samu dabaru masu yawa da kwararrun jami'ai don cimma nasarar aiwatar da shirin.

Kasar Afrika ta kudu na son amfani da yankunan raya tattalin arziki na musammam, wajen gaggauta bunkasa ayyukan masana'antu da ci gaban tattalin arziki da magance rashin aikin yi da fatara. (Fa'iza Mustapha)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China