Ministan kimiyya da fasaha na kasar Afrika ta kudu Mmamoloko Kubayi-Ngubane, shi ne ya sanar da hakan, wanda kuma ya halarci bikin a jami'ar fasaha ta Cape Peninsula University of Technology (CPUT) dake birnin Cape Town, inda za'a aika da tauraron dan adam din zuwa Indiya, inda daga can ne kuma za'a harba tauraron a watan Yuli.
Tauraron dan adam din mai nauyi kilogram 4, wanda aka fi sani da ZACUBE-2, jami'ar ta CPUT ne ta kera shi tare da hadin gwiwar cibiyar nazarin fasaha ta French South African Institute of Technology.
Za'a yi amfani da tauraron dan adam din wajen bincike a tekun Afrika ta kudu da kuma gano wutar daji ta hanyar na'urar daukar hoto wanda cibiyar nazari da binciken kimiyya ta (CSIR) ta kera. (Ahmad Fagam)