Wannan ita ce tawagar wakilan gwamnati ta farko da gwamnatin kasar Sin ta tura zuwa kasar Burkina Faso tun bayan da aka farfado da dangantakar diflomasiyya tsakanin kasashen biyu a ran 26 ga watan Mayun bana. Wannan ya bayyana cewa gwamnatocin kasashen biyu na muhimmanta dangantakar dake tsakanin kasashen biyu.
Lu Kang ya kara da cewa, bisa gayyatar da gwamnatin kasar Sin ta yi masa, shugaba Christian Kaboré na Burkina Faso zai halarci taron kolin dandalin tattaunawar hadin gwiwa tsakanin Sin da Afirka da za a yi a watan Satumban bana a birnin Beijing na kasar Sin. (Sanusi Chen)