in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kasashen Sin da Afrika ta kudu sun shirya bikin wasannin fasaha a Pretoria
2017-04-26 19:54:08 cri

A daren jiya ranar Talata ne a Pretoria, aka shirya bikin wasannin fasaha don murnar soma gudanar da tsarin cudanyar al'adu a tsakanin kasashen Sin da Afrika ta kudu, da bikin cika shekaru 23 da kafa sabuwar kasar Afirka ta kudu. 'Yan wasa da suka fito daga kungiyar kundunbala, kungiyar sufaye masu wasan Kungfu na kasar Sin, da na kungiyar raye-rayen Vuyani ta Afirka ta kudu, da kuma masu rera wakokin kasashen biyu ne suka nishadantar da mahalarta.

Mataimakiyar firaministan kasar Sin Liu Yandong, ministan fasaha da al'adun kasar Afirka ta kudu Nathi Mthethwa da kuma wakilan kasashen biyu da suke halartar taron farko na tsarin cudanyar kasashen biyu da bukukuwan da batun ya shafa ne suka kalli wasannin. (Bilkisu)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China