in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
MDD: Mahaukaciyar guguwa da ruwan sama ta halaka mutane 16 a Somaliya
2018-05-21 19:28:25 cri
Ofishin kula da harkokin jin kai na MDD (OCHA) ya sanar a yau Litinin cewa, a kalla mutane 16 ne suka mutu, bayan da wata mahaukaciyar gugu dake tafe ruwan sama kamar da bakin kwarya mai suna Saga ta ratsa yankin Somaliland dake arewacin Somaliya a karshen mako.

Ofishin OCHA ya kuma ce, ambaliyar ruwa ta yiwa dubban jama'a da ma kayayyakin more rayuwa barna, baya ga wadanda suka rasa mutsugunansu.

Mahaukaciyar guguwar mai tafe ruwan sama ta haifar da mummunan yanayin jin kai a jihohin Somaliland da Puntland da ma wasu yankunan da ake takaddama a kansu, inda suka fuskanci fari a shekarar 2015.

Rahotanni daga yankin na cewa, kwale-kwalen kamu kifi da dama sun bace a yankin. Koda yake masana hasashen yanayi na cewa, karfin mahaukaciyar guguwar yana raguwa., inda yanzu ta doshe wasu sassan Habasa, Djibouti da arewa maso yammacin Somaliland.(Ibrahim)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China