in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
OCHA: Ambaliyar ruwa ta raba mutane 220,000 da muhallansu a Somaliya
2018-05-12 15:37:05 cri
Ofishin kula da harkokin jin kai na MDD(OCHA) ya bayyana a jiya Jumma'a cewa, kimanin mutane 220,000 ne suka rasa matsugunansu, sakamakon barnar da kogunan Juba da Shabelle ke ci gaba da yi bayan da suka tumbatsa biyo bayan ruwan sama mai karfin gaske da aka tabka.

Mataimakin kakakin hukumar ta OCHA Jens Laerke, ya bayyanawa zaman MDD cewa, ambaliyar ta shafi mutane 718,000 a yankin arewa maso gabashin Afirka,yayin da mutane 132 suka mutu a Kenya.

Laerke ya ce, abokan hulda masu gudanar da ayyukan jin kai da hukumomi Somali suna samar da kayayyakin taimakon rai, taimakon na'urorin sauko da mutane zuwa kasa, da raba buhunan kasa don gyara gabobin kogin da suka lalace. Haka kuma, ana tsammanin ci gaba da fuskantar ambaliyar ruwa a wasu yankuna a kasar Habasha.

A watan Afrilu kadai, kimanin mutane 171,000 ne suka rasa matsugunansu a sassan kasar, galibi saboda ambaliyar da ta faru a yankin Somali.(Ibrahim)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China