in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Shugaba Macky Sall ya bayyana ziyarar da shugaba Xi zai gudanar a Senegal a matsayin mai muhimmanci ga sassan biyu
2018-07-21 15:10:54 cri
Shugaban kasar Senegal Macky Sall, ya bayyana ziyarar da shugaba Xi Jinping zai gudanar a Senegal, a matsayin mai muhimmancin gaske ga tarihin alakar sassan biyu.

Shugaba Sall, wanda ya bayyana hakan yayin zantawa da wata kafar watsa labarai ta kasar Sin a ranar Alhamis, ya ce alakar kasashen biyu ta samu kyautatuwa a 'yan shekarun baya bayan nan, inda tuni aka fara cin gajiyar hakan ta hanyar kammala manyan ayyuka, yayin da wasu kuma ke ci gaba da gudana a yanzu haka.

Shugaba Sall ya ce kasarsa na alfahari da karbar bakuncin shugaba Xi, wanda shi ne shugaban Sin na farko da zai kai ziyara kasar cikin shekaru 9, kuma kasar ta Senegal ce zangon shugaban na farko a yammacin Afirka, tun bayan kama aikinsa a matsayin shugaban kasar Sin a karo na biyu.

Ya ce Sin da Senegal sun riga sun daga matsayin kawance su bisa matsayin koli, ta hanyar hadin gwiwa da juna, za kuma su ci gaba da inganta wannan nasara, karkashin tsarin kyautata dangantakar Sin da kasashen Afirka.

Ana dai sa ran yayin zaiyarar da shugaban na Sin zai kai Senegal, shugabannin kasashen biyu za su sanya hannu kan yarjejeniyoyin hadin gwiwa da dama. Kuma tuni shugaba Sall ya bayyana fatan ganin Sin ta kara shiga a dama da ita, a harkokin da suka shafi tsare tsaren raya kasar ta Senegal. (Saminu Hassan)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China