in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Ziyarar Shugaban kasar Sin a kasar Senegal za ta karfafa alakar kasashen biyu, in ji jakadan Sin
2018-07-21 14:29:58 cri
Jakadan kasar Sin a Senegal Zhang Xun, ya bayyana cewa, ziyarar da shugaban kasar Sin Xi Jinping zai gudanar a kasar Senegal, za ta daga matsayin alakar kasashen biyu zuwa wani sabon mataki, wanda zai kasance mai alfanu ga al'ummun su.

Jakada Zhang ya kara da cewa, a 'yan shekarun baya bayan nan, kyakkyawar alakar dake akwai tsakanin Senegal da Sin na kara inganta, inda tuni sassan biyu suka fara amfana da sakamakon dangantakar tasu. An kuma gudanar da ayyukan hadin gwiwa da dama, yayin da yanzu haka ake ci gaba da aiwatar da wasu sabbin ayyukan yadda ya kamata.

A daya hannun kuma, kasashen biyu na karfafa amincewar juna ta fuskar siyasa, da kuma alakar dake akwai tsakanin Sin da kasashen Afirka.

A cewar Mr. Zhang, ya zuwa karshen shekarar 2017, yawan jarin da kasar Sin take da shirin zubawa a Senegal ya kai dalar Amurka miliyan 320. Kana yawan jarin da Sin ta riga ta zuba a kasar kai tsaye ya kai dalar Amurka miliyan 110, adadin da ya karu da kaso 120 bisa dari bayan shekara guda.

Har ila yau a cikin shekaru 3 a jere, yawan cinikayya tsakanin sassan biyu ya kai dala biliyan 2, wanda hakan ya sanya Sin ta kasance kasa mafi girma ta 2 a duniya, a yawan gudanar da cinikayya da Senegal.

Jakadan na Sin ya kuma jaddada cewa, ko shakka babu Sin da kasar Senegal, za su ci gaba da karfafa zumunta da hadin gwiwa, za kuma su bullo da sabbin dabarun kyautata hadin kai, ta yadda za su ci gajiya daga salon kyautata fasahohin samar da makamashi, da yawon shakatawa, da sufurin jiragen sama. (Saminu Hassan)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China