Wata sanarwa da Tarayyar ta fitar jiya Juma'a, ta ce shugaban hukumar kula da ayyukanta Moussa Faki Mahamat, ya tura jami'an ne biyo bayan gayyatar da gwamnatin kasar dake yammacin Afrika ta mika Tarayyar, kuma jami'an za su kasance a kasar daga ranar 22 ga watan Yuli zuwa 4 ga watan Augusta.
An zabo jami'an ne daga cikin mambobin kwamitin wakilai na dindin-din na AU da majalisar dokokin tarayyar da hukumomin kula da zabe da kungiyoyin al'umma dake aiki kan harkokin da suka shafi demokuradiyya da shugabanci da zabuka a Afrika da masana da kuma masana harkokin zabe masu zaman kansu. (Fa'iza Mustapha)