A yayin bikin, an yi nune-nunen littattafai 1589 da aka fassara su daga Sinanci zuwa harshen Faransanci. Abubuwan dake kunshe cikin wadannan littattafai sun shafi harkokin siyasa, tattalin arziki, al'adu da dai sauransu na kasar Sin. Sannan an kuma kafa wani dandali na musamman, inda aka yi nune-nunen littattafai game da shugaba Xi Jinping na kasar Sin, kamar littafi na farko da na biyu game da batun mulkin kasa da tafiyar da harkokin siyasa, da irin jawaban da shugaba Xi Jinping ya gabatar a yayin wasu muhimman bukukuwan kasa da kasa. Bugu da kari, an kuma yi nune-nunen wasu littattafai game da babban burin da kasar Sin take kokarin cimmawa, da hanyoyin neman ci gaba da kasar Sin take bi, da ilimomin jam'iyyar kwaminis ta kasar Sin da shawarar "ziri daya da hanya daya", ta yadda al'ummomin kasar Senegal za su iya kara sani da kuma fahimtar kasar Sin ta yanzu yadda ya kamata. (Sanusi Chen)