Rahoton daya ne daga cikin abubuwan da aka bayyana a dandalin shugabannin siyasa game da shirin ci gaba mai dorewa da ke gudana a halin yanzu, wanda ke bitar ajandar da MDD ke fatan cimmawa nan da shekarar 2030, game da manufofin ci gaba mai dorewa guda 17.
A cewar rahoton, an yi kiyasin cewa daga shekarar 2010 zuwa 2050, za a samu karuwar al'umma biliyan 2.5 zuwa 3 kan yawan al'ummar dake zaune a birane a fadin duniya.
Rahoton ya kuma yi hasashe game da samun bunkasuwa a yankuna marasa ci gaba, kamar yankunan gabashi da kudancin Asiya da kasashen Afirka dake kudu da hamadar sahara. (Ibrahim Yaya)