in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Mutane a kalla 10 sun mutu sakamakon ambaliyar ruwa a Ghana
2018-06-22 13:24:57 cri
Kakakin hukumar kula da iftila'i na kasar Ghana, ya ce mutane a kalla 10 sun mutu sakamakon ruwan sama da aka yi ba dare ba rana a baya bayan nan.

Rahotanni na cewa, tun a ranar 18 ga wata aka fara ruwan sama a Ghana, abun da ya haddasa ambaliyar ruwa a wurare daban-daban. Daga cikinsu, ambaliyar ta fi yawa a birnin Accra, inda gine-gine da dama suka lalace, al'amarin da ya tilastawa mazauna da dama kaura.

Kwararru a kasar sun bayyana cewa, yanayin shimfidar kasa a Accra ya yi kasa sosai, sannan rashin kyan tsarin magudanan, baya ga wasu gine-gine da aka yi ba bisa ka'ida ba, da bola da suka toshe magudanan ruwa, sun kara tsananta halin da ake ciki.

Jami'in ya ce hukumar ta bukaci gwamnati da gyara magudanan ruwan tare da rushe wadancan gine-gine don tinkarar iftila'in. (Amina Xu)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China