in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
MDD: Akwai bukatar inganta jagoranci a hukumar zaben kasar Ghana
2018-07-06 11:09:09 cri

Jakadiyar MDD a kasar Ghana Christine Evans-Klock, ta jinjinawa kwazon gwamnatin Shugaba Nana Addo Dankwa Akufo-Addo, bisa yadda take ci gaba da nada jami'an da suka cancanta, a hukumar zaben kasar ba tare da wani jinkiri ba, a wani mataki na tabbatar da nasarar ayyukan hukumar na nan gaba.

Uwargida Evans-Klock, wadda ke jagorantar ofishin tsare tsare na MDDr dake Ghana, ita ce ta bayyana hakan cikin wata sanarwa, tana mai cewa, majalissar ta gamsu da matakan da ake dauka, wajen tantancewa, da kuma nada mukamai a hukumar zaben kasar ta Ghana, ciki hadda sanya dukkanin sassan masu ruwa da tsaki daga jam'iyyu daban daban, da kuma jam'iyyun gama kai na al'umma a tsarin jagorancin hukumar.

Jami'ar ta kara da cewa, irin tallafi da MDD ke baiwa wannan hukuma domin cimma nasarar ayyukan tana da matukar tasiri, kuma za a ci gaba da aiwatar da hakan a nan gaba.

A ranar Alhamis ne dai Shugaba Addo Dankwa Akufo-Addo, ya sauke jagoran hukumar zaben kasa Charlotte Osei daga mukaminsa. Hakan kuwa ya biyo bayan karbar sakamakon bincike da wani kwamiti mai mutane 5, wanda mai shari'a Sophia Akuffo ta kafa, domin bin bahasin wasu korafe korafe da aka yi, kan wasu manyan jami'an hukumar zaben kasar su 3.

Rahoton ya gabatar da shawarar tube jami'an daga mukamansu ne, bayan da kwamitin binciken da aka kafa ya tabbatar da zargin da aka yi musu, na nuna halayyar rashin cancanta, da kuma karya ka'idojin gudanar da ayyukan hukuma.(Saminu Alhassan)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China