in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Rundunar 'Yansanda Ta Kama Wadanda Suka Sace 'Yanmatan Chibok
2018-07-20 22:16:17 cri

Mu samu labari daga shafin Intanat na Leadershipayau kan cewa, Rundunar 'yansanda ta jihar Borno ta kama mutum 22 wadanda ake zargin 'yan kungiyar Boko Haram ne, sun kuma hada da wadanda suka sace 'yan makarantar 'yanmata ta garin Chibok. Kwamishinan 'yansanda na jihar CP Damian Chukwu shi ne ya bayyana hakan, lokacin da yake gabatar da wadanda aka ga manema labarai, jiya a Maiduguri, ya bayyana cewar takwas daga wadanda ake zargin kungiyar Boko Haram ne, da kuma manyan kwamandojinsu wadanda suke da hannu a al'amarin satar 'yan matan makarantar Chibok, da kuma hare-hare fiye da 50 da aka kai Maiduguri da kuma wasun sassa na Adamawa.

Kamar dai yadda wata sanarwar da aka fitar wadda kuma take dauke da sa hannum kwamishinan 'yansanda, data bayyana cewar daga cikin wadanda aka kama kuma ake tsare da su, akwai wadanda suke da hannu cikin mamayar da aka kai ma garin Bama da kuma Gwoza, da kuma hare haren da aka kai ma akan Hukumomin tsaro, da kuma farar hula a sashen Arewa maso gabas.

Chukwu ya kara jaddada cewar su kame kamen an yi su ne cikin makonni biyu da suka wuce, a jhohin Borno da kuma Yobe, kafin a kai ga dawo da IGP bangaren Intelligence Respond Team (IRT) karkashin shugabancin DCP Abba Kyari.

Wadanda ake zargi da aikata laifin sun hada da manyan kwamandojin uku, masu samar da kayayyaki biyu, sai kuka mayaka goma sha bakwai.

Ya kuma bayyan sunayen wadanda suke da hannu wajen sata da kuma karguwa da 'yan matan makarantar Chibok, akwai mutum mai shekara 23 wanda ake kira da suna Mayima Madu wanda aka fi sani da Abor, Adam Muhammad 29,Gujja Jidda21, da kuma Mamman Mardi mai shekara 23. Sauran sun hada da Madu Jidda 29, Ajun Bulama Dungas 22, Muhammad Abba 20, da kuma Fannanu Mustafa 22.

Chukwu ya kara jaddada cewar su wadanda ak zargi da aikata laifin, sun amsa cewar lallai sun aikata laifin da ake zarginsu, musamman ma satar 'yan makarantar mata na Chibok, sun kuma shugabanci wasu hare-haren da aka kai.

Bugu da kari kuma ita sanarwar tayi bayani akan wani mutum wanda ake kira da suna Adam Mustapha mai shekaru 20, wanda shi ne ya shugabanci wasu hare haren kunar bakin wake a Maiduguri da kuma Adamawa, bayan haka kuma ya bayyana cewar, shi ne ke jagoranta da kuma kai 'yan kunar bakin wake mata da maza, ya fito da su daga dajin Sambisa, zuwa wuraren da suke kai hare haren tsakanin jihohin Adamawa da kuma Borno.

Daga cikinn bayanan sun hada da '' shi wanda ake zargin ya amsa laifin cewar shi ne, ya jagoranci hare haren da aka kai hanyar Baga, Bulunkutu, Custom, Postoffice, 3-3 housing, da kuma Mina area a Maiduguri, su wadannan hare haren sun kasance sanadiyar rasa rayuka masu yawa da kuma kaddarori. Shi ma wanda ake zargi da aikatan laifin Mustapha Kanimba wanda aka fi sani da Alaramma, mai shekaru 20, wanda shi kuma dan asalin Mobbar Bomo, shi yana da ga cikin 'yankungiyar Boko Haram kuma kwamnada ne wanda yake samar da kayayyaki ya kai zuwa dajin Sambisa, ya kuma ce ya shiga cikin wasu haren haren da aka kai, wadanda kuma an kashe daruruwan mutane a Maiduguri. Yayin da shi kuma Ibrahim Mala mai shekaru 48 dan asalin karamar hukumar Gwoza ne ta jihar Borno, wanda ya zauna unguwannin Dalori da kuma karekare a cikin Maiduguri, shi ne ke kai 'yan kungiyar kayayyakin abinci da kuma wasu kayayyaki.

Bayanan kwamishinan 'yansandan bai manta da akwai auran 'yan kungiyar wadanda suka hada da Abdullahi Muhammad Gawi 23, Maina Adam 35, Wano Musa 23, Ishaka Musa 26, Abubakar Muhammed 29, Usman Umar 28, Maina Umar 27, Maina Gambo 24, Abubakar kari 25, da kuma Bukar Abacha 39. Hakanan ma akwai dan shekara 35 Muhammad Bashir wanda aka fi sani da, kalijango, shi kuma dan asalin Gamboru Ngala, shi kuma dan kungiyar cibilian JTF ne, wato kungiyar hadin kai ta farar hula, shi ma an kama shi saboda yana taimakawa su 'yan kungiyar Boko Haram wajen kai masu kayayyaki.

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China